Isa ga babban shafi
Ghana-Najeriya

Bamu saba ka'ida ba kan laftawa 'yan kasuwar Najeriya haraji

Gwamnatin Ghana ta hannun ministan yada labaran ta Kojo Nkrumah tace ko kadan bata saba ka’ida ba wajen lafta harajin dala miliyan 1 kan ‘yan Najeriya dake kasuwanci a kasar, da wasu karin sabbin dokoki da suka shafe su.

Ministan yada labaran Ghana Kojo Oppong Nkrumah
Ministan yada labaran Ghana Kojo Oppong Nkrumah REUTERS/Kweku Obeng NO RESALES. NO ARCHIVES.
Talla

Yayin kare matakin, ministan yada labaran na Ghana yace abin mamaki ne matuka yadda wasu, musamman Najeriya ke bayyana matakai, ko dokokin da kasar ta kafa a matsayin wuce gona da iri, la’akari da cewar gwamnatin Najeriya ta sha daukar matakan da suka na kasar ta Ghana tsauri don kare manufofinta.

Nkrumah yace daya daga cikin tsauraran matakan da Najeriya ta dauka a baya bayan nan shi ne rufe iyakokinta da makwaftan kasashe daga watan Agustan 2019 har zuwa wannan lokaci, matakin da janyowa makwaftan nata koma bayan tattalin arziki.

Ministan yada labaran na Ghana, ya kuma zargi ‘yan kasuwa baki musamman na Najeriya da karya dokokin kasuwanci, gami da almundahana, ciki harda kin biyan haraji, rashin cika ka’idojin zaman bakunta, da kuma saida kayayyaki marasa inganci.

A makon da ya kare, ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed ya sha alwashin gwamnatin Najeriya ba za ta cigaba da sa ido kan yadda gwamnatin Ghana ke cin zarafin ‘yan Najeriyar dake kasar ba, ciki harda matsawa ‘yan kasuwa da kuma tilasta maida ‘yan Najeriyar akalla 825 gida cikin shekara 1, yayinda wasu kuma aka yanke musu hukunce hukunce dauri masu tsauri.

Sai dai Ghana ta kare kanta da cewar, dukkanin matakan da ta dauka bai sabawa doka ba, la’akari da cewar nata dokokin, da manufofi aka bijirewa, wanda kuma ya zama dole ta magance matsalarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.