Isa ga babban shafi
Najeriya

Abin fashewa ya halaka mutane a Katsina

Fashewar wani abu da ake zaton bam ne a jihar Katsina dake Najeriya, yayi sanadin mutuwar mutane dakalla 5 tare da jikkata wasu.

Taswirar kasar Najeriya dake nuna jihar Katsina.
Taswirar kasar Najeriya dake nuna jihar Katsina. Photo/Gamers
Talla

Majiyoyi da dama sun ce fashewar ta auku ne da safiyar yau Asabar, a wata gona dake kauyen ‘Yammama a karamar hukumar Malumfashi.

Kakakin ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah yace kawo yanzu mutane 5 ‘ya’ya ga wani Alhaji Adamu aka tabbatar da mutuwarsu, koda yake wasu shaidun gani da iso sun ce mutane 6 suka mutu, yayinda wasu 6 suka jikkata.

Dukkanin wadanda suka rasa rayukan nasu dai yara ne, wadanda suka je gonar domin diban ciyawar dabbobi.

Katsina na daga cikin jihohin arewacin Najeriya masu fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga dake halaka rayukan jama’a, da kuma satar mutanen don karbar kudin fansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.