Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Farfesa Shehu Abdullahi Zuru kan bukatar zartas da hukuncin kisa kan 'yan bindiga da kwamitin Noma na majalisar wakilan Najeriya ya gabatar

Wallafawa ranar:

Shugaban Kwamitin Noma a Majalisar Wakilan Najeriya Mukhtar Dan Dutse ya bukaci sanya hukuncin kisa kan 'yan bindigar da suka addabi yankin Arewacin kasar da kuma makiyayan da ke kashe manoma.Dan Majalisar ya ce rashin daukar mataki mai tsauri kan irin wadannan mutane na barazanar jefa Najeriya cikin yunwa ganin yadda manoma suka kauracewa gonakin su saboda fargabar hallaka su.Dangane da wannan matsayi, mun ji ta bakin masanin shari’a Farfesa Shehu Abdullahi Zuru na Jami’ar Abuja, kuma ga tsokacin da yayi akai.

Wasu 'yan bindiga a Najeriya.
Wasu 'yan bindiga a Najeriya. Daily Trsut
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.