Isa ga babban shafi
Najeriya

Binciken Magu alama ce muna yakar matsalar rashawa da gaske - Gwamnatin Najeriya

Alkalumman hukumomin lafiya da kamfanin dillancin labarai na AFP ya tattara, sun nuna cewar annobar coronavirus da ta halaka sama da mutane dubu 565 daga cikin kusan miliyan 13 da suka kamu, na dada yin karfi a maimakon sauki, tun bayan shiga watan Yuli da muke ciki.

Wani tsohon hoton shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da korarren shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu.
Wani tsohon hoton shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da korarren shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu. Sahara Reporters
Talla

Sanarwar da kakakin shugaban Najeriya malam Garba Shehu ya fitar, tace wadanda suke kallon binciken da ake yiwa Magu a matsayin gazawar ta wajen magance matsalar ta cin hanci, sun yi kuskure.

Fadar gwamnatin Najeriyar ta kuma ce babu wanda ya fi karfin fuskantar hukunci bisa laifin da ya aikata, komai kusancinta da shi, ciki kuwa harda tsohon shugaban na EFCC, wanda tace ta bashi damar kare kansa da tuhume-tuhumen da yake fuskanta na sace wani kaso na makudan kudaden da aka kwato daga mahandama.

A ranar Juma’ar da ta gabata shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar da matakin dakatar da Ibrahim Magu daga shugabancin EFCC a hukumance, ‘yan kwanaki bayan gurfana gaba kwamitin bincike kan zarge-zargen almundahanar makudan kudade.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.