Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan Najeriya sama da dubu 11 sun warke daga cutar coronavirus

Hukumar yaki da yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC, ta ce an samu karin mutane 454 da suka kamu da cutar coronavirus a ranar Juma’a, abinda ya kai jumillar adadin zuwa dubu 27 da 564.

Ma'aikatan wani kamfanin samar da sinadarin tsaftace hannu a jihar Legas dake Najeriya. 19/3/2020.
Ma'aikatan wani kamfanin samar da sinadarin tsaftace hannu a jihar Legas dake Najeriya. 19/3/2020. REUTERS/Temilade Adelaja
Talla

Daga cikin jihohi 18 da aka samu karin wadanda suka kamun, Legas ke kan gaba da mutane 87, sai Edo mai 63, Abuja na da 60, 41 a Ondo.

Zuwa yanzu mutane dubu 11 da 69 suka warke daga cutar a Najeriya, yayinda 628 suka mutu.

Akalumma dai sun nuna cewar kusan watanni biyar bayan bullar annobar coronavirus a Najeriya, Legas ke kan gaba tsakanin jihohin kasar wajen yawan wadanda suka kamu da cutar da adadin mutane dubu 10 da 910, biye kuma birnin Abuja ne da mutane dubu 2 da 80, sai kuma jihar Oyo mai mutane dubu 1 da 451.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.