Isa ga babban shafi

Korona ta tsananta fyade a Najeriya - 'Yan Sanda

Sufeto Janar na Yan Sandan Najeriya Muhammadu Adamu yace a cikin watanni 5 da suka gabata an samu mutane 717 da suka yiwa mata fyade a kasar, matakin dake dada nuna yadda ake cin zarafin mata a kasar.

Sufeto Janar da 'yan sandan Najeriya Mohammed Adamu
Sufeto Janar da 'yan sandan Najeriya Mohammed Adamu Vanguard.ng
Talla

Yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan lamarin, Sufeto Janar Adamu yace yanzu haka rundunar sa na tsare da mutane 799 da ake zargi da aikata wannan laifi daga cikin laifuffuka 631 da aka gabatar musu kuma suka mika kotuna.

Adamu yace jami’an sa na cigaba da gudanar da bincike kan wasu zarge zarge 52 dake da nasaba da fyaden, inda ya bukaci Yan Najeriya da su taimaka su wajen basu bayanai da kuma shaidun da zasu taimaka musu wajen gudanar da ayyukan su da kuma hukunta wadanda ake zargi.

Sufeto Janar din ya danganta karuwar matsalar fyade da killace jama’a da akayi a gidajen su domin yaki da annobar COVID-19, abinda ya dada fito da matsalar fili.

Ko a makon jiya sanda kungiyoyin kare hakkin mata da wasu na fararen hula suka yi ta shelar ganin anyi doka mai karfi wajen yaki da fyade a Najeriya saboda ganin yadda matsalar ke karuwa a fadin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.