Isa ga babban shafi

An sanya dokar hana fita a wasu yankunan Adamawa

Gwamnatin Jihar Adamawa dake Najeriya ta sanya dokar hana fita na sa’oi 24 a garuruwan Lafiya da Boshikiri da Zakawan da Masermi da Dumna da Zerbu da Dumna Burthi da Dumba Dutse da duwu da Tsaibu dake kananan hukumomin Lamurde da Guyuk sakamakon tashin hankalin da aka samu.

'Yan sandan Najeriya
'Yan sandan Najeriya RFI HAUSA
Talla

Sanarwar da Humwashi Wonosikou ya sanyawa hannu a madadin Gwamnan Jihar ta umurci mazaunanan wadanan yankuna da su mutunta dokar yayin da jami’an tsaro ke sintiri domin tabbatar da zaman lafiya.

Jihar ta Adamawa dai ta sha fama da rikicin kabilanci a baya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama,ko a ranar 15 ga watan Mayun ta ta gabata, rundunar 'yan sandar jihar ta tabbatar da ɓarkewar rikicin ƙabilanci a wani kauye na jihar.

Rikicin ya barke ne tsakanin Hausawa mazauna garin Tinno da kabilar Chobo da ke karamar hukumar Lamorde, inda akayi fargabar cewa mutane da dama sun rasa rayukansu a cikin rikicin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.