Isa ga babban shafi
Coronavirus

Najeriya: Sama da mutane 500 sun kamu da coronavirus a rana 1

A karon farko tun bayan bullar annobar coronavirus a Najeriya watanni 3 da suka gabata, sama da mutane 500 sun kamu da cutar cikin kasar a rana guda.

Daya daga cikin kayayyakin gwajin cutar Coronavirus.
Daya daga cikin kayayyakin gwajin cutar Coronavirus. Reuters
Talla

Akalumman da cibiyar dakile yaduwar cutuka ta Najeriya a daren rana Asabar sun nuna cewar, karin mutane 553 gwaji ya tabbatar sun kamu da cutar coronavirus, adadi mafi yawa da kasar ta gani a rana guda.

Har yanzu yanzu kuma Legas ce jihar da wannan annoba ta fi karfi a cikinta, la’akari da cewar ita ke kan gaba wajen yawan sabbin mutanen da suka kamu a ranar ta Asabar, da adadin mutane 378, sai Abuja mai mutane 52, Delta 23, Edo 22, Ogun 13, sai Kaduna 12, yayinda karin mutane 9 suka kamu da cutar a Kano.

Sauran jihohin da aka samu karin mutanen da cutar ta coronavirus ta kama sun hada da, Borno mai mutane 7, katsina 6, Jigawa da Oyo 5-5, Yobe da Filato 3-3, yayinda Osun ke da mutum 1.

Kawo yanzu jumillar mutane dubu 9 da 855 gwaji ya tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Najeriya, sai dai dubu 2 da 856, yayinda wasu 273 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.