Isa ga babban shafi
Najeriya

Dogaran tsohon babban hafsan tsaron Najeriya sun taka rawa wajen mutuwarsa - Bincike

Rundunar sojin saman Najeriya ta sanar da kammala bincike kan wasu jami’anta 6, da take tuhuma da yin sakacin da ya kai ga kisan tsohon babban hafsan tsaron kasar Air Chief Marshal Alex Badeh.

Tsohon babban hafsan tsaron Najeriya Air Chief Marshal Alex Badeh a Abuja, 20/1/2014.
Tsohon babban hafsan tsaron Najeriya Air Chief Marshal Alex Badeh a Abuja, 20/1/2014. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Cikin sanarwar da ta fitar a Juma’ar da ta gabata, rundunar sojin saman Najeriyar tace kotun ta bisa jagorancin mai shari’a Air Comodore David Aluku, ta samu masu tsaron lafiyar marigayi Badeh guda shida, da laifukan da suka hada da, gujewa ayyukansu da gangan, bada shaidar karya, da kuma amfani da makamai ko harsasan rundunar sojin saman ba bisa ka’ida ba.

A watan Disambar shekarar 2018, wasu ‘yan bindiga suka harbe tsohon babban hafsan tsaron Najeriya Alex Badeh, kan hanyar Abuja zuwa Keffi, lokacin da yake komawa gida daga gonarsa.

An kashe Badeh ne a dai dai lokacin da yake fuskantar tuhuma kan zargin karkatar da kudaden sayen makamai.

A yanzu haka dai kotun sojin saman ta mike binciken nata zuwa ga mataki nag aba, domin fayyace makomar masu tsaron lafiyar marigayi Badeh bisa laifukan da aka tabbatar akansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.