Isa ga babban shafi
Coronavirus

Ganduje ya sassauta dokar hana fita a Kano

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da sassauta dokar hana fitar da gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa a ranar 27 ga Afrilun da ya gabata, don yakar annobar coronavirus.

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. RFIHAUSA/Abubakar Isa Dandago
Talla

Yayin sanar da matakin sassauta dokar, Ganduje ya bayyana litinin da kuma alhamis, a matsayin ranakun da jama’a za su rika fita, amma daga karfe 10 na safe zuwa karfe 4 na yamma.

Gwamna Ganduje yace kasuwannin ‘Yan Kaba da kuma Rijiyar Lemo kawai ne za su rika budewa a daukacin jihar, yayinda sauran manyan shagunan saida kayayyaki za su cigaba da harkokinsu a ranakun da gwamnati ta baiwa jama’a damar fita.

Daga ranar litinin 4 ga watan Mayu sassaucin dokar hana fitar a Kano zai soma aiki.

A ranar Alhamis 30 ga watan Afrilu, gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya roki gwamnatin tarayyar Najeriya da ta sassauta dokar hana fita ta tsawon makwanni 2 da ta kafa a jihar, domin dakile yaduwar annobar coronavirus.

Ganduje yace sassauta dokar kullen, zai saukakawa al’ummar jihar halin matsin da suka shiga sakamakon tsayar hada-hadar kasuwanci, ayyuka, da sauran harkokin yau da kullum.

Matakin gwamnan na Kano ya zo ne sa’o’i bayan sanarwar da kungiyar likitocin Najeriya NMA ta fitar, dake bayyana matakin sassauta dokar hana fita a jihohin Legas da Ogun da kuma birnin Abuja a matsyin kuskure, la’akari da karuwar adadin masu dauke da cutar coronavirus a kasar, gami da karancin adadin jama’ar da ake yiwa gwajin cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.