Isa ga babban shafi
Najeriya

Sanwo-Olu ya zayyana sharuddan sassauta dokar hana fita a Legas

Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya bayyana jerin matakan da gwamnatin jihar za ta dauka wajen sassauta dokar hana fitar da ta shafe sama da makwanni 4 tana aiki, domin dakile yaduwar annobar coronavirus.

Wani yankin birnin Legas, yayinda dokar hana fita ke aiki, domin dakile yaduwar annobar coronavirus.
Wani yankin birnin Legas, yayinda dokar hana fita ke aiki, domin dakile yaduwar annobar coronavirus. AFP/Getty Images
Talla

Sanwo-Olu ya bayyana matakan ne yayin jawabin da ya gabatar a larabar nan kan sauyin da aka yiwa dokar hana zirga-zirgar da aka kafawa al'ummar jihar a baya.

A matakin farko, gwamnan ya bada umarnin cewa daga yanzu, dukkanin motocin dakon abinci da sauran albarkatun noma daga sassan Najeriya, za su rika shiga da fita daga jihar dauke da fasinjojin da ba za su zarta adadin mutane 7 ba, saboda bankado shirin bata gari dake boye fasinjoji a motocin dakon daukar kaya.

A bangaren kasuwanni kuma gwamnan na Legas yace za a rika bude kasuwannin da sauran shagunan saida kayayyaki daga karfe 9 na safe zuwa 3 na yammaci a wasu zababbun ranaku, zalika ya zama tilas a kiyaye tsaftar muhalli da ta jiki yayin hada-hadar kasuwanci.

Sanwo-Olu ya kuma sanyawa dukkanin shagunan saida kayayyaki dokar takaita yawan mutanen da za su baiwa damar shiga cikinsu, da adadin kashi 60 cikin 100 da za su iya dauka, zalika dole mutanen su nisanci juna da tazarar akalla mitoci 2.

Gwamnan birnin na Legas ya kuma ce daga ranar litinin mai zuwa, 4 ga watan mayu, dukkanin fasinjojin ababen hawa musamman na haya, tilas su rika sanya kyallayen rufe baki da hanci, zalika motocin bas za su rika daukar kashi 60 cikin 100 na adadin fasinjojin da suke da ikon dauka a baya, domin kiyaye cinkoson jama’a.

Dukkanin wuraren Ibada kuma za su cigaba da kasancewa a rufe har sai abinda hali yayi.

Dangane da ma’aikatan gwamnati kuma, Babajide Sanwo-Olu ya baiwa dukkanin wadanda ke kan matakin daraja ta 12 zuwa kasa, umarnin gudanar da ayyukansu daga gida, sai dai in bukatar zuwa ofisoshinsu ya zama tilas. Su kuma ma’aikatan dake matakin daraja ta 13 zuwa sama, za su rika gudanar da ayyukansu a ofisoshi  tare da kiyaye sharadin nisantar juna.

Matakin sassauta dokar haramta fita baki dayan dai zai soma aiki a jihohin Legas, Ogun da kuma Abuja daga ranar 4 ga watan Mayu, kamar yadda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umarni.

A karkashin sauyin, za a rika fita harkokin yau da kullum a jihohin ne daga karfe 6 na safe zuwa 8 na dare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.