Isa ga babban shafi
Najeriya

Za mu dauki mataki kan farmakin Katsina-Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce, za a dauki matakin da ya dace game da harin baya-bayan nan da wasu ‘yan bindiga suka kai kan mazauna karkara a jihar Katsina, inda suka kashe mutane 47.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. businessday
Talla

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, Garba Shehu, shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da harin wanda aka kai a kauyukan kananan hukumomi  Danmusa da Dutsinma da kuma Safana a ranar Asabar.

Buhari ya ce, ba zai laumci salwantar da rayukan al’umma da barayi ke yi ba, yayin da ya umarci hukumomin tsaro da su kara zage dantse don ganin cewa, tsargerun ba su samu sararin kai hare-hare ba.

Sashen Hausa na RFI ya tattauna da Kakakin Rundunar ‘Yan sandan jihar Katsina DSP Gambo Isah kuma ya yi cikakken bayani kan farmakin.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirarsa da Abdulkarim Ibrahim Shikal.

03:35

Hira ta musamman da kakakin 'yan sandan Katsina kan harin 'yan bindiga

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.