Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun kashe mutane kusan 50 a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina da ke Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 47 a wani hari da ‘yan bindiga suka kaddamar kan wasu kauyuka da ke jihar.

Mazauna karkarar sun yi kukan-kura tare da samun nasarar fatattakar 'yan bindiga
Mazauna karkarar sun yi kukan-kura tare da samun nasarar fatattakar 'yan bindiga Jakarta Globe
Talla

‘Yan bindigar sun hallaka jama’a a kauyukan da ke kananan hukumomin Danmus da Dutsinma da Safana, yayin da mutane da dama suka jikkata a harin na ranar Asabar.

Farmakin ya tilasta wa dimbin jama’a kaurace wa muhallansu.

Kodayake wasu rahotani sun ce, mazauna karkarar sun yi kukan-kura inda suka yi nasarar fatattakar ‘yan bindigar, yayin da suka yi ta kona karmami don nuna wa barayin cewa, lallai suna farke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.