Za mu iya kera wa Najeriya na'urar Ventilator- Matasa
Wasu matasan injiniyoyi sun gyara na’urorin taimaka wa mara lafiya yin numfashi da ake kira Ventilator a harshen Turanci a asibitin koyarwa na jami’ar Jos da ke jihar Filaton Najeriya duk da cewa, a karon farko kenan da suka yin ido biyu da na’urorin.
Wallafawa ranar:
Fasahar matasan ta kayatar da hukumomin asibitin ganin cewa, babu wanda ya zaci cewa, matasan za su iya gyara na’urorin.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da karancin ire-iren wadannan na’urori a fadin Najeriya duk da cewa ana matukar bukatar su musammam a wannan lokacin da annobar coronavirus ke harbar mutane.
Matasan sun bayyana cewa, za su iya taimaka wa gwamnatin Najeriya ta hanyar kera ire-iren wadannan na'urorin.
Matasan da suka gyara na'urar Ventilator a Najeriya
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu