Isa ga babban shafi
Najeriya

An samu karin mutane 3 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya

Hukumomin lafiya a Najeriya sun ce an samu karin mutane 3 da suka kamu da cutar murar Coronavirus da ta zamewa duniya annoba.

Wata mai ziyarar mara lafiya a asibitin sojin Najeriya na 68 dake Legas, a lokacin da ake bincikar zafin jikinta.
Wata mai ziyarar mara lafiya a asibitin sojin Najeriya na 68 dake Legas, a lokacin da ake bincikar zafin jikinta. AFP / Getty Images
Talla

Hakan na nufin karuwar adadin mutanen da annobar ta shafa a kasar zuwa 25. Sai dai jami'an lafiya sun tabbatar da warkewar 2 daga cikin marasa lafiyar.

Cibiyar bincike da dakile yaduwar cutuka ta Najeriya tace an tabbatar da samun karin mutane ukun ne da safiyar yau lahadi, dukkaninsu kuma a birnin Legas.

Bincike ya tabbatar da cewar cikin makon da ya gabata, baki dayan marasa lafiyar sun yi balaguro zuwa kasashen Turan dake fama da annobar murar.

A ranar asabar 21 ga watan maris cibiyar binciken cutukan Najeriyar ta sanar sake samun mutane 10 da suka kamu da cutar coronavirus, abinda a waccan lokacin ya kai adadin mutanen da suka kamu a kasar zuwa 22.

Cibiyar yaki da cututtuka ta sanar da cewar daga cikin sabbin mutane 10 da suka kamu da cutar, 7 na Lagos ne, yayin da guda 3 kuma ke zama a Abuja.

Cibiyar tace 9 daga cikin masu dauke da cutar sun dawo ne daga tafiya zuwa kasashen waje, yayin da guda daga cikin su kuma ya samu cutar wajen mu’amala da wadanda ke dauke da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.