Isa ga babban shafi
Najeriya

Musulmai sun kaurace wa Masallatan Juma'a a Lagos

Kamar yadda mahukuntan jihar Lagos ta Najeriya suka bayar da umarni, a yau juma’a mafi yawan masallatai sun kasance a rufe a birnin don hana yaduwar cutar Coronavirus wadda ta kashe mutane sama da dubu 10 a sassan duniya. 

Coronavirus ta tilasta wa hukumomin Lagos rufe Masallatan Juma'a don hana yaduwar cutar
Coronavirus ta tilasta wa hukumomin Lagos rufe Masallatan Juma'a don hana yaduwar cutar JOHANNES EISELE / AFP
Talla

Sheikh Abdullahi Imam Haris, shi ne limamin masallacin juma’a na Owo Street da ke unguwar Agege, ya ce tabbas sun karbi umarnin da hukumomi suka ba su, domin kuwa ba su yi sallar juma’ar ba.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraran bayanin da Sheik Abdullahi ya yi wa RFI Hausa.

01:04

Muryar Sheikh Abdullahi kan rufe masallatan Juma'ar Lagos

Kodayake wasu rahotannin sun ce, an samu tsirarun Masallatan da suka gudanar da sallar Juma'a a jihar duk da umarnin da mahukunta suka bayar na rufe Masallatan da Coci-coci.

Masana kiwon lafiya sun ce, cinkoso dimbin jama'a na daya daga cikin hanyoyin yada cutar Coronavirus wadda ta zama ala-ka-kai ga duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.