Isa ga babban shafi
Najeriya-Coronavirus

Gwamnatin Legas ta hana tarukan Ibada saboda Coronavirus

Gwamnatin Jihar Lagos dake Najeriya ta sanar da dakatar da Sallar Juma’a da kuma addu’oin lahadi da ake gudanarwa a mujami’un kasar domin dakile yaduwar cutar coronavirus.

Taron jama'a a wani yankin birnin Legas.
Taron jama'a a wani yankin birnin Legas. Reuters / Akintunde Akinleye
Talla

Kwamishinan dake kula da harkokin cikin gida na Jihar Anofiu Elegushi ya bayyana haka bayan wani taron da gwamnatin Jihar tayi da malaman addinai wanda ya amince da cewar a kaucewa duk wani taron da ya wuce na mutane 50.

Elegushi yace hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta tababtar da cewar taron jama’a na daga cikin abinda key ada cutar, saboda haka ya zama wajibi a dauki mataki kamar yadda kasashen duniya suka dauka.

Kwamishinan yace an kafa kwamitin da zai sa ido domin tabbatar da aiwatar da dokar daga bangarorin Musulmi da Kirista.

Taron da aka yi da shugabannin addinin ya kuma baiwa gwamnatin shawarar rufe iyakokin ta na kasa da sama domin hana baki shiga kasar.

Babban limamin Lagos, Oluwatoyin Abou-Nollah da shugaban kungiyar kiristoci Alexander Bamgbola sun yaba da matakin da gwamnatin Jihar ta dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.