Isa ga babban shafi

Bani da hannu a tube sarki Sanusi na II - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya musanta duk wata masaniya dangane da tube sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari RFI Hausa
Talla

Babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga shugaban kasa Mallam Garba Shehu ne ya bayyana hakan Laraban nan ta shafin sa na twitter.

Wannan na zuwa ne bayan da tsohon gwamnan Kano, Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso ya dora alhakin tube Sarkin Muhammadu Sanusi na II kan shugaba Muhammadu Buhari.

A watan da ya gabata shugaban Najeriyar ya bayyana dalilansa na kin tsoma baki a rikicin Ganduje da Sarki Sanusi na II.

A ganawar shugaba Muhammadu Buhari da tawagar gwamnatin Kano da ta kunshi wasu sabbin ‘yan majalisu karkashin jagorancin gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, shugaban kasar ya bayyana wasu daga cikin dalilin da ya hana shi tsoma baki a rikicin Gwamnan da Mai martaba sarki Muhamamdu Sanusi na II.

Buhari ya bayyana cewa karkashin kundin tsarin mulkin kasa, ba shi da hurumin tsoma baki a rikicin la’akari da yadda batun ke gaban Majalisar Jihar, matakin da ke nuna cewa Gwamnan na Kano Abdullahi Ganduje tare da Majalisar ne kadai ke da ta cewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.