Isa ga babban shafi

Miyatti Allah ta rasa damar shiga AMOTEKUN

Majalisun Dokokin Jihohin dake Kudu maso Yammacin Najeriya sun ki amincewa da bukatar kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah na shiga ayyukan sabuwar kungiyar tsaron da suka samar ta Amotekun.

Kungiyar tsaron da jihohin Kudu masu Yammacin Najeriya ta Amotekun.
Kungiyar tsaron da jihohin Kudu masu Yammacin Najeriya ta Amotekun. RFI/Hausa
Talla

Shugabannin Miyetti Allah sun shaidawa taron bainar jama’a da Majalisar dokokin Jihar Oyo tayi, cewar suna goyan bayan kafa rundunar tsaron kuma suna bukatar sanya ‘yayan su, amma hakan bai yiwu ba.

Shugaban Majalisar dokokin Jihar Oyo Olayanju Qozeem yace ko duba bukatar kungiyar ta miyetti Allah ba su yi ba, domin babu dalilin yin haka, yayin da Majalisar Jihar Osun tace bata samu irin wannan bukata daga kungiyar ba.

Wani rahota da Jaridar Premium Times da ake wallafawa a Najeriya tayi, yace tuni Majalisun suka kamala aiki kan samar da dokar ba tare da amincewa da bukatar kungiyar Fulanin ba.

A ranar alhamis, shugabannin Majalisun dokokin jihohin sun gudanar da wani taro a Ibadan domin daukar matsayin bai daya kan yadda dokar zata yi aiki.

Ana saran kwamishinonin shari’a daga jihohin yankin su gudanar da taron su makon gobe kafin amincewar Majalisun da kuma mikawa gwamnonin domin rattaba hanu akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.