Isa ga babban shafi
Najeriya

An yi wa mata sama da 600 fyade a Sokoto a bara

Hukumar Hisbah ta jihar Sokoto a Najeriya ta koka kan yawaitar matsalar cin zarafin mata, tana mai cewa, ta tattara alkaluma 606 na fyade da aka yi kananan yara mata a bara kadai.

Akasarin matan da ake yi wa fyaden ba su wuce shekara 5 zuwa 16 ba a Sokoto
Akasarin matan da ake yi wa fyaden ba su wuce shekara 5 zuwa 16 ba a Sokoto Daily Trsut
Talla

Shugaban Hukumar ta Hisbah, Dr. Adamu Bello Kasarawa ya bayyana haka,inda ya ce, matsalar ta zarta wadda aka gani a shekarar 2018, lokacin da aka tattara alkaluma 296 na fyaden.

A cikin watan Janairun bana, Hukumar ta samu korafin fyade har sau 31, abin da ke nuna kazancewar matsalar.

Akasarin matan da ake yi wa fyaden ba su wuce shekara 5 zuwa 16 ba a cewar shugaban na Hisbah.

Daga cikin masu aikata fyaden har da ‘yan siyasa da sarakunan gargajiya da limamai da attajiran 'yan kasuwa maza da mata kamar yadda Dr. Kasarawa ya yi karin bayani.

Jami'in ya bukaci gwamnatin Sokoto da ta tallafa wa Hukumar ta Hisbah da kayan aiki kamar motoci domin yakar matsalar fyade da sauran ayyukan assha a jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.