Isa ga babban shafi
Najeriya

Ganduje da Tambuwal sun yi nasara a kotun kolin Najeriya

Kotun Kolin Najeriya ta kori karar da Abba Kabiru Yusuf ya shigar a gabanta, yana kalubalantar nasarar da Abdullahi Umar Ganduje ya samu a zaben gwamnan da aka gudanar a watan Maris na 2019, yayin da kotun ta dauki makamancin wannan matakin na tabbatar da sahihancin zaben Aminu Tambuwal a matsayin gwamnan jihar Sokoto bayan ta yi watsi da karar da Ahmed Aliyu ya shigar,inda ya kalubalanci sahihancin zaben.

Ganduje da Tambuwal
Ganduje da Tambuwal Sahara Reporters
Talla

A wani hukunci na bai-daya da alkalai biyar karkashin jagorancin Sylvester Ngwuta suka yanke, kotun kolin ta ce, Kabiru Yusuf na PDP da Ahmed Aliyu na APC sun gaza gabatar da shaidun da ke nuna cewa, an yi san-kai a hukuncin farko da kotun daukaka kara ta dauka na tabbatar da nasarar Ganduje da Tambuwal.

Gabanin zaman kotun nay au, rahotanni sun tabbatar cewa, ana zaman dari-dari a jihohin biyu, amma kawo yanzu babu wani bayani da ke nuna cewa, an samua hatsaniya.

A makon jiya ne kotun kolin karkashin jagorancin Alkalin-Alkalai, Tanko Muhammed ta dage zaman yanke hukuncin zuwa yau.

Lauyan da ke kare dan takarar gwamann Kano karkashin jam’iyyar PDP, Abba Kabiru Yusuf Gida-Gida, ya bukaci kotun kolin da tsauya hukuncin kotun daukaka kara tare da tabbatar da wanda ya ke karewa a matsayin wanda ya yi nasara a zaben na ranar 9 ga watan Maris na bara.

Lauyan ya ce, Baturen Zabe a jihar Kano ya bi haramtacciyar hanya wajen soke sakamakon zaben rumfuna 207 a jihar, inda ya bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba, sannan ya ayyana ranar 23 ga watan Maris a matsayin ranar sake kada kuri’u a wasu rumfuna, matakin da jam’iyyar PDP ta bayyana da magudi.

Shi ma lauyan Ganduje ya bukaci kotun kolin da ta yi watsai da karar da PDP ta shigar tare da tabbatar da wanda yake karewa a matsayin wanda ya yi nasara a zaben.

Haka ma dai wannan rikicin siyasar yake a jihar Sokoto, inda APC ke fatan kotun kolin ta sauya nasarar da Tambuwal ya samu, amma PDP ta bukaci kotun da ta yi watsi da korafe-korafen da APC ta shigar saboda rashin makama ballantana tushe a cewarta.

Rahotanni na cewa, wasu daga cikin jiga-jiran gwamnati daga Kano da Sokoto sun koma Abuja gabanin zaman yanke hukuncin na yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.