Isa ga babban shafi
Najeriya-Adamawa

Boko Haram ta farmaki garin Michika na jihar Adamawa

Rahotanni daga Jihar Adamawa sun bayyana cewa hare-haren kungiyar Boko Haram cikin yammacin jiya Alhamis ya tilastawa kauyuka da dama tserewa zuwa cikin birane.

Dakarun Sojin Najeriya bayan nasarar kwace iko da garin Damasak.
Dakarun Sojin Najeriya bayan nasarar kwace iko da garin Damasak. REUTERS/Emmanuel Braun
Talla

Wata majiya ta ce da misalign karfe 6 na yammacin jiya ne mayakan na Boko Haram suka shiga karamar hukumar Michika tare da farmakar kauyukan Kwuapale da Kwuapa har ma da Baza.

Wasu faya-fayan bidiyo da al’ummar karamar hukumar ta Michika suka wallafa sun nuno yadda mutane ciki har da mata da kananan yara ke bi ta kan duwatsu don ketarawa zuwa Yola babban birnin Jihar ta Adamawa.

Yayin farmakin na Boko Haram wanda suka shafe kusan sa’o’I 6 rike da yankin babu wasu bayanai da ke nuna kai daukin jami’an tsaro a karamar hukumar ta Michika haka zalika babu bayanan da ke nuna an rasa rayuka.

Harin na Michika ya zo ne a dai dai lokacin da ake shirin cika shekara guda da makamancin hari kan karamar hukumar ranar 28 ga watan Maris na shekarar 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.