Isa ga babban shafi
Najeriya

Zamfara ta daina biyan tsoffin gwamnoni fansho

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara da ke Najeriya ta amince da dokar soke biyan kudaden fansho na tsoffin gwamnoni da mataimakansu da kuma shugabannin majalisu sakamakon korafe-korafen da dokar ta haifar.

Gwaman jihar Zamfara, Bello Matawalle
Gwaman jihar Zamfara, Bello Matawalle premiumtimesng
Talla

Mai magana da yawun majalisar, Mustapha Jafaru ya ce, dan majalisar da ke wakiltar mazabar Maradun, Faruk Dosara ya gabatar da kudiri a kai, wanda ya samu goyan bayan Tukur Birnin Tudu daga Bakura, abin da ya bai wa Majalisar damar tafka mahawara a kai.

Jami’in ya ce, bayan da shugaban majalisar Nasiru Magarya ya bayar da izinin tattaunawa kan kudirin, an masa karatu na farko da na biyu, kafin majalisar ta yi zama na kwamiti a kansa.

Jafaru ya ce, daga nan aka yi wa kudirin karatu na uku kuma aka amince da shi ya zama doka.

Jami’in ya ce, nan gaba za a mika wa gwamnan Jihar, Bello Matawalle domin rattaba hannu akai.

Yin dokar ya biyo bayan wasikar da tsohon gwamna Abdulaziz Yari ya rubuta wa gwamna Matawalle, inda yake bukatar ya biya shi kudaden fanshonsa na naira miliyan 10 a kowanne wata, wanda ya ce sau biyu kawai aka biya shi tun bayan saukarsa daga mukamin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.