Isa ga babban shafi

Kungiyar agaji ta ACF ta tabbatar da kame jami'anta 6 a Najeriya

Kungiyar agaji ta Action Against Hunger (ACF) mai rajin yaki da yunwa musamman a yankunan da rikici ya daidaita ta tabbatar da yin garkuwa da jami’anta 6 a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Shugaban tsagin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga kungiyar IS Abu Musab Al-Barnawi
Shugaban tsagin kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga kungiyar IS Abu Musab Al-Barnawi Guardian Nigeria
Talla

Sanarwar kungiyar ta ACF da ke zuwa bayan fitar faifan bidiyon kungiyar jihadi da ke tabbatar da kame jami’an 6, ta ce tana aiki da hukumomin Najeriya wajen ganin mutanen sun baro hannun ‘yan ta’adda cikin koshin lafiya.

Cikin sanarwar ta kungiyar ACF da ke da babban Ofishinta a kasar Faransa, ta ce jami’an sun shiga Najeriya ne da nufin kai dauki da mutanen da ke cikin tsananin yunwada talauci sanadiyyar rikicin Boko Haram.

A safiyar yau Alhamis ne, kungiyar wadda ke biyayya ga IS ta fitar da faifan bidiyon da ke nuna mutanen 6 rike a hannunta.

Cikin faifan biyon na tsawon minti 3 da kungiyar jihadin ta saki a yau, an sanyo wata mata guda sanye da hijabi mai launin shudi da aka bayyana da jami’ar agajin na jawabi cikin harshen turancin Ingilishi a gefenta kuma da wasu maza guda 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.