Isa ga babban shafi
Najeriya

Zamfara: Majalisar Sarakuna ta bukaci katse layukan sadarwa

Majalisar koli ta Sarakunan gargajiyar jihar Zamfara, ta bukaci gwamnatin Najeriya ta kafa tawaga ta musamman don gudanar da bincike kan hare-haren ‘yan bindiga a jihar, domin zakulo wadanda ke da hannu, da kuma tabbatar da cewa an hukuntasu.

Wani gida da 'yan bindiga suka kone a wani farmaki da suka kai kan kauyen Kizara, da ke jihar Zamfara a Najeriya.
Wani gida da 'yan bindiga suka kone a wani farmaki da suka kai kan kauyen Kizara, da ke jihar Zamfara a Najeriya. AFP
Talla

Shugaban majalisar Sarakunan gargajiyar, kuma Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmad ne ya gabatar da bukatar a fadarsa, lokacin da ministan harkokin cikin gidan Najeriya Laftanar Janar AbdulRahman Dambazau mai ritaya ya kai ziyara.

Sarkin ya kuma bukaci gwamnati ta dauki matakin katse layukan sadarwa a jihar, musamman a yankunan da ke fama da hare-haren na ‘yan bindiga zuwa wani lokaci, matakin da ya ce zai taimaka matuka wajen dakile kokarin da wasu bata gari ke yi, wajen sanar da maharan shirye-shiryen da jami’an tsaro ke yi na murkushe su.

Baya ga katse layukan sadarwar Sarkin na Anka ya bukaci tsaurara matakan tsaro kan dukkanin hanyoyin da mahara ke bi wajen kaiwa jama’a farmaki, zalika a damke duk wanda aka gani yana kai kawo a yankunan.

Ministan cikin gidan na Najeriya ya ziyarci jihar ta Zamfara ce bisa umarnin shugaba kasar Muhammadu Buhari, kwanaki kalilan bayan da ‘yan bindiga suka tilasta wa jama’ar karamar hukumar Shinkafi da ke jihar ta Zamfara a kwana cikin daji sakamakon farmakin da suka kai musu da tsakiyar dare, inda suka yi awon gaba da akalla mutane 40 da suka hada da ‘yan kasar Ghana.

A waccan lokacin yayin zantawa da sashin Hausa na RFI, Dakta Sulaiman Shu’aibu Shinkafi, Sarkin Shanun Shinkafi ya bayyana takaicinsa kan yadda jami’an sojoji suka ki kawo musu dauki a yayin farmakin har sai da 'yan bindigar suka ci karensu babu babbaka.

Bayan watsa rahoton na sashin Hausa na RFI, gwamnatin Najeriya ta aike da sojoji masu yawan gaske zuwa karamar hukumar ta Shinkafi, kamar yadda Sarkin Shanun na Shinkafin Dakta Suleiman Shu’aibu ya tabbatar mana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.