Isa ga babban shafi
Najeriya

Oshoimhole ya zargi INEC da yiwa APC rashin adalci

Shugaban APC mai mulkin Najeriya Adams Oshoimhole, ya zargi hukumar zaben kasar INEC da yi wa jam’iyyar zagon kasa yayin gudanar da manyan zabukan kasar na 2019 da aka kammala.

Shugaban Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Adams Oshiomole.
Shugaban Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Adams Oshiomole. Daily Post
Talla

Yayin manyan zabukan Najeriya dai, APC ce ta lashe zaben shugaban kasa, inda shugaba Muhammadu Buhari yayi nasarar samun wa’adi na biyu, zalika jam’iyyar ta APC ce ke kan gaba wajen yawan kujeru a majalisun dokokin kasar na Wakilai da Dattijai.

Sai dai duk da haka, Oshoimhole ya zargi INEC da yi wa APC rashin adalci, wanda ya ce ya fara tun daga yadda hukumar ta rika daukar matakai kan zabukan jam’iyyar na fitar da gwani a wasu jihohi, kamar Zamfara da Rivers.

Oshoimhole ya kara da cewa yayin gudanar da manyan zabukan da aka kammala, INEC ta cutar da APC a jihohin da take da rinjaye, ta hanyar bada damar kada kuri’a ba tare da yin amfani da na’urar tantance masu kada kuri'a na Card Reader ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.