Isa ga babban shafi
Najeriya

Dan takarar NRM ya nemi kotu ta soke takarar Buhari da Atiku

Dan takarar shugabancin Najeriya na jam’iyyar NRM Usman Ibrahim Alhaji, ya garzaya kotu inda ya shigar da karar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da dan takarar PDP Atiku Abubakar bisa karya dokar kashe kudade fiye da ka’ida yayin yakin neman zabensu.

Dan takarar shugabancin Najeriya na jam’iyyar NRM Usman Ibrahim Alhaji
Dan takarar shugabancin Najeriya na jam’iyyar NRM Usman Ibrahim Alhaji uia.org.ng
Talla

Ibrahim Alhaji ya bukaci babbar kotun tarayyar ta soke takarar Buhari da Atiku a zaben shugaban kasar da ya gudana a ranar 23 ga watan Fabarairu, saboda laifin da suka aikata na karya dokar zaben najeriya ta shekarar 2010.

Mai shigar da karar ta hannun lauyansa mai suna, Ofou Ezekiel, ya zargi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar dan takarar PDP da kashe sama da naira biliyan 1, yayin yakin neman zabensu, matakin da ya ce saba shi, zai bada damar soke cancantar takararsu a zaben shugabancin Najeriya na bana da aka kammala.

Bayan sauraron koken, mai shari’a Muhammed, ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 26 ga watan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.