Isa ga babban shafi
Najeriya-Zamfara

'Yan bindiga sun kai sabon hari a garuruwan Zamfara

Wasu ‘yan bindiga sun kaddamar da sabbin hare-hare a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, in da suka kashe mutane da dama tare da kona gidajensu a garuruwan da ke karkashin karamar hukumar Gusau.

Jihar Zamfara na fama da hare-haren barayin shanu
Jihar Zamfara na fama da hare-haren barayin shanu shakarasquare
Talla

Mazauna yankin sun shaida wa sashen Hausa na RFI cewa, jami’an tsaro sun gaza ba su kariya duk da cewa, an tura wani jirgin saman soji da ya dauki lokaci yana shawagi a yankin da aka kai farmakin.

Jami'an tsaron sun bukaci mazauna yankin da su yi ta kansu kamar yadda rahotanni ke cewa.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren wani bangare na abin da mazauna yankin suka shaida mana.

01:03

Sabbin hare-haren jihar Zamfara

Kawo yanzu ba a tabbatar da adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba a hare-haren na baya-bayan nan, amma rahotanni na cewa, daga cikin wadanda aka kashe har da ‘yar uwar Sanata Kabiru Marafa da maharan suka yi awon gaba da mijinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.