Isa ga babban shafi
Najeriya

Mazauna Baga da Doro sun tsere daga muhallansu - Rahoto

Hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar Borno a Najeriya SEMA, ta ce sama da mutane dubu 10 sun tsere cikin mako guda, daga garuruwan Baga, Doro, da kuma wasu kauyuka 10, da ke karamar hukumar Kukawa domin kaucewa farmakin mayakan Boko Haram.

Wasu 'yan gudun hijira da hare-haren Boko Haram ya raba da muhallansu a Najeriya.
Wasu 'yan gudun hijira da hare-haren Boko Haram ya raba da muhallansu a Najeriya. AFP
Talla

Shugabar hukumar ta SEMA, Hajiya Yabawa Kolo, ta shaidawa manema labarai a garin Munguno cewa, dubu 7 daga cikin ‘yan gudun hijirar, da suka kunshi manoma da masunta a yanzu haka suna garin na Munguno, yayin da wasu kimanin dubu 2 da 900 suka isa Maiduguri.

Yayin ziyarar da ya kai garin na Munguno a jiya Asabar, gwamnan jihar ta Borno kashin Shettima, ya ce zuwa yanzu an mika tallafin abinci da sauran kayayyakin bukata zuwa Munguno dauke cikin manyan motoci 30, wadanda za a rabawa ‘yan gudun hijira sama da dubu 250 da ke zaune a sansanoni 12 da ke garin.

A gefe guda kuma, rundunar sojin Najeriya na ci gaba da shirin afkawa mayakan Boko Haram, domin karbe garin na Baga, da wasu kauyukan da rahotanni suka ce mayakan sun mamaye a arewacin jihar ta Borno.

Rahotannin dai sun ce mayakan na Boko Haram, bangaren shugabancin Abu Mus’ab Albarnawi ne suka mamaye yankunan, bayan fafatawa da dakarun Najeriya a makon da ya gabata, sai dai sojin Najeriyar sun ce janye wa suka yi bisa radin kansu, domin bada damar kwashe fararen hula daga yankunan, kafin yin amfani da cikakken karfi wajen murkushe mayakan na Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.