Isa ga babban shafi
Najeriya

INEC ta gargadi jam’iyyu kan wa’adin zabukan fidda gwani

Hukumar shirya zaben Najeriya, INEC, ta gargadi jam’iyyun kasar da cewa, ba zata tsawaita wa’adin ranar 7 ga watan Oktoba mai zuwa da ta sanya a matsayin ranar karshe ta gudanar da zaben fidda gwanin ‘yan takara ba.

Wasu ma'aikatan hukumar zaben Najeriya, yayin kokarin isa rumfunan zaben dake garin Otuoke, a jihar Bayelsa. 28 ga Maris, 2015.
Wasu ma'aikatan hukumar zaben Najeriya, yayin kokarin isa rumfunan zaben dake garin Otuoke, a jihar Bayelsa. 28 ga Maris, 2015. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Babban jami’in hukumar zaben, kuma shugaban kwamitinta mai kula da sashin ilimintar da masu kada kuri’a, Solomon Soyebi, ya ce hukumar ta yanke hukuncin ne a taron da ta yi ranar Alhamis a garin Abuja.

Soyebi ya kara da cewa, INEC ba zata sauya ranar 18 ga watan Oktoba a matsayin wa’adin karshe na mika takardun ‘yan takarar da jam’iyyu suka tsayar a zaben shugabancin Najeriya ba.

Zalika har yanzu ranar 2 ga watan Nuwamba ce, wa’adin karshe na mika takardun ‘yan takarar kujerun gwamnoni, ‘yan majalisun tarayya, da na ‘yan majalisun jihohi da jam’iyyu suka tsaida ba.

Sanarwar da hukumar zaben ta fitar ranar Alhamis a birnin Abuja, ta ce tana dakon sakamakon wadannan zabubuka daga jam’iyyun siyasar kasar 89 daga cikin 91 da ta yiwa rijista.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.