Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun kashe fararen hula 35 a Adamawa-Amnesty

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce wani hari da rundunar sojin saman Najeriya ta kai cikin watan Disamban da ya gabata, ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 35 a wasu kauyuka da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin kasar.

Al'ummar arewacin Najeriya sun fuskanci kazamin hare-hare na Boko Haram
Al'ummar arewacin Najeriya sun fuskanci kazamin hare-hare na Boko Haram Médecins sans Frontières (MSF) / AFP
Talla

Rahotan na Amnesty ya ce a ranar 4 ga watan Disamba jirgin sojin sama ya kai harin gargadi kan kauyukan da ake yawaita samun rikici Fulani da makiyaya, wanda kungiyar ke cewa kai hari ba hanyar ba ce ta samar da doka da oda.

Kakakin sojin saman Najeriya Olatokubo Adesanya, ya musanta wannan bayanin, to sai dai ya ce wani lokaci a baya, dakarunsu sun kai farmaki a kan wasu da ake zargi da barnata da dukiyar jama’a a yankin.

Bayan shafe shekaru na gaza daukan matakai a rikici tsakanin Makiyaya da Manoma, lamarin a yanzu ya kazance wanda ke barazanar ga tsaron kasar.

Amnesty dai ta yi gargadin cewar wannan rikici na da hatsarin gaske, yayin da kasar ke kokarin kawo karshen ayyukan mayakan Boko Haram.

Darakta kungiyar a Najeriya, Osai Ojigho, ta ce a cikin watan Janairu kawai an kashe mutane 168 a rikice-rikicen da aka samu a Jihohin Adamawa da Benue da Taraba da Ondo da kuma Kaduna, yayin da gwamnati ta gaza wajen kare rayukan jama’a.

Mrs. Osai ta ce wasu lokuta jami’an tsaro kan yi amfanin da karfin da ya wuce kima waje kashe mutane maimakon shawo kan rikicin, kuma ba’a hukunta masu aikata laifufuka.

Gwamantin Shugaba Muhammadu Buhari na yawaita fuskantar suka kan gaza kawo karshan wannan rikici tsakanin Fulani da makiyaya ko hukunta masu hannu a tada zaune tsayen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.