Isa ga babban shafi
Najeriya

Rundunar sojan Najeriya ta 93 ajihar Benue ta kama mutane 9 dauke da bindigo kirar AK47

Rundunar Sojin a bataliya ta 93 dake garin Takun na jihar Taraba a tarayyar Najeriya ta kama mutane 9, daga cikinsu guda 5 na dauke da bindigogi, a wani gari da ke kan da iyakar jihohin Benue da Taraba inda ake fama da rikice rikicetsakanin manoma damakiyaya.

Wasu  yan bindiga da aka kama da makamai sun ce gwamnatin Benue ce ta daukesu aiki
Wasu yan bindiga da aka kama da makamai sun ce gwamnatin Benue ce ta daukesu aiki Faceboock
Talla

Binciken da sojojin suka gudanar a kan mutanen, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar Benue ce ta dauke su aiki. A zantawar da Muka yita wayar telefon shugaban bataliyar, Kanar Babatunde Gambari ya bayyana cewa: “ A shekaranjiya 7 ga wannan wata najanairu, akwai sojoji da muka tura domin tabbatar da tsaro sakamakon wasu bayanai da ke cewa, akwai wasu mutane dauke da makamai, lokacin da jami’anmu suka isa can ne suka gano wadannan mutane su 9, biyar daga cikinsu kowanne na da bindiga kirara AK47, jami’anmu sun bukaci su ajiye makamansu ko kuma su dauki matakin da ya dace akansu. Daga nan ne kuma aka zo da su zuwa bataliyarmu da ke Takun domin bincike.

RFI Hausa: Bayan gudanar da wannan bincike, mi kuka gano akansu kuma daga ina suka fito?

Kanar Babatunde Gambari: Binciken da muka gudanar sun tabbatar mana da cewa, su na yi wa gwamnatin jihar Benue aiki ne, ita ta dauke su ta kuma ba su horo kan yadda ake sarrafa bindiga, kuma an dauke su ne tun watan junin shekarar bara wato kafin fara aiki da dokar hana kiwo a watan nuwambar bara.

RFI Hausa: Wa ye, ya dauke su aiki?

Kanar Babatunde Gambari: Sun tabbatar mana da cewa gwmanatin jihar Benue ce ta dauke su kuma tana biyansu albashi duk da cewa, yau watanni biyar kenan ba ta biya su ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.