Dan kunar bakin wake ya kashe mutane 50 a Masallacin Mubi
Kimainin mutane 50 sun rasa rayukansu bayan wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam din da ke jikin sa a cikin wani Masallaci da ke garin Mubi a jihar Adamawa ta Najeriya.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rahotanni na cewa, maharin ya tayar da bam din ne a Masallacin Madina da ke Unguwar Shuwa a dai dai lokacin da jama’a suka hallara don gudanar da sallar Asuba a safiyar yau Talata.
Shugaban karamar hukumar Mubi ta Arewa, Musa Bello ya ce, yanzu haka ana kan tattara alkaluman mutanen da harin ya shafa amma ya tabbatar da asarar rayukan da aka samu.
Mr. Bello ya ce, tuni aka garzaya da wadanda suka samu rauni zuwa asibiti.
Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhaki harin amma mayakan Boko Haram sun sha kai hare-hare a Adamawa musamman a can baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu