An cafke kwamandan kungiyar IS a Kano
Hukumar jami’an tsaron farin kaya ta DSS, ta cafke wani kwamandan reshen kungiyar IS, reshen Afrika ta yamma, Haussieni Mai-Tangaran a garin Kano, da ta dade tana farautarsa.
Wallafawa ranar:
Hukumar ta ce Mai Tangaran ne ya shirya mafi akasarin muggan hare-haren da mayakan Boko Haram suka kai a sassan Najeriya, ciki harda mummunan harin a aka kai a garin Kano, na ranar 20 ga watan janairun shekara ta 2012.
Zalika hukumar ta DSS, ta ce Mai Tangaran ne ya shirya kai harin ta’addancin da ya hallaka daruruwan mutane, yayinda suke gabatar da Sallar Juma’a a masallacin gidan sarki a Kano, sai kuma harin da aka kaiwa barikin sojoji a jihar Yobe a shekarar 2015.
Kakakin hukmar ta DSS Tony Puiyo ya ce, sun kuma lalata shirin ‘yan ta’adda na kai muganna hare-hare a biranen Najeriya musamman a Lokacin bikin Sallah babba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu