Isa ga babban shafi
Najeriya

Za'a sauya Yan Sandan da ke aiki a titin Abuja zuwa Kaduna

Sufeto Janar na Yan Sandan Najeriya Ibrahim Idris ya bada umurnin sauya daukacin Yan Sandan da su ke aiki akan hanyar Abuja zuwa Kaduna domin kawo karshen matsalolin rashin tsaron da ake samu.

Jami'an Yan sanda na musamman masu yaki da fashi da makami da kuma garkuwa da mutane.
Jami'an Yan sanda na musamman masu yaki da fashi da makami da kuma garkuwa da mutane. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Kakakin rundunar Yan Sandan Jimoh Moshood yace matakin zai shafi jami’ai daga masu matsayin kwamandan shiyya zuwa kurtu da ke aiki a wannan Yanki.

Hanyar Abuja zuwa Kaduna dai ta zama wani dandalin ayyukan ta’addanci da suka hada da fashi da makami da sace mutane don karbar kudi a matsayin diyya.

Sufeto Janar din Yan Sandan Najeriyar Ibrahim Idris, ya bukaci kwamishinonin Yan Sandan Abuja da Niger da kuma Kaduna su tashi tsaye wajen ganin an kawo karshen matsalolin tsaron da suka jefa jama’a da dama cikin tashin hankali a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.