Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya zata samu agajin dala miliyan 121 daga Amurka

Najeriya na cikin kasashe 4 da Amurka ta alkawarta bai wa tallafin Dala miliyan 639 don ciyar da mutane da ke fama da yunwa sakamakon fari da yake-yake.

Shugaban Amurka Donald Trump na rangadi a Turai
Shugaban Amurka Donald Trump na rangadi a Turai REUTERS/Kacper Pempel
Talla

A cikin kudadden da shugaba Donald Trump na Amurka ya umarci a ware don rabawa kasashen da suka hadar da Somalia da Sudan ta Kudu da Yemen, Najeriya zata samu dala Miliyan 121.

Wani Jami’in Ma’aiakatar ci gaban kasashe ta USAID da ke Amurka, Rob Kenkins, da ke tabbatar da agajin ya ce za a warewa Yemen dala Miliyan 191.

Kana Sudan ta Kudu zata samu agajin dala miliyan 199, sai Somalia da za a ware mata dala Miliyan 126.

Mista Jefkins, ya ce da wannan sabon agajin, Amurka zata sake samar da Karin kayayyakin abinci a cikin gaggawa da magunguna, kana za a inganta tsafta da samar da wadatattun matsugunai da bada kariya tare da inganta rayuwar wadanda yaki ya tagayara.

Jami’in ya kuma shaida cewa, USAID, ta damu da halin da ake ciki a kudancin Habasha, don haka Amurka ta ware dala miliyan 252 don taimakawa kasar a cikin wannan shekarar, sai dai a koda yaushe bukatun na sake girma.

Taimakon Amurka na zuwa ne bayan taron G20 da aka kammala a birnin Hamburg na Jamus

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.