Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: An kame madugun kungiyoyin sata da garkuwa da mutane

Rundunar 'yan sandan Najeriya, ta samu nasarar kama wani kasurgumin mai sata da kuma garkuwa da mutane a birnin Legas, bayan shafe lokaci mai tsawo tana nemansa ruwa a jallo.

Mutumin da rundunar 'yan sandan Najeriya ta shafe tsawon lokaci tana nemansa ruwa a jallo, saboda rawar da ya dade yana takawa, wajen shugabantar wasu gungun masu sata da garkuwa da mutane.
Mutumin da rundunar 'yan sandan Najeriya ta shafe tsawon lokaci tana nemansa ruwa a jallo, saboda rawar da ya dade yana takawa, wajen shugabantar wasu gungun masu sata da garkuwa da mutane. The Nation Nigeria
Talla

Shugaban rundunar yan sandan ta musamman da aka fi sani da IRT, ACP Abba Kyari, ya shaidawa kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN cewa, mai laifin da ke amsa sunan Evans, wanda suka shafe tsawon lokaci suna nema ruwa a jallo, sun damke shi ne, a wani gidansa da ke Magodo a birnin Legas.

ACP Kyari, yace, mutumin ya kwashe akalla shekaru 7 yana shugabantar gungun masu sata da garkuwa da mutane daban daban, wadanda sukai nasarar amshewa mutane da dama biliyoyin nairori kafin sakin wadanda suka sace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.