Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamitin sasantawa da 'yan majalisa

Fadar shugaban kasar Najeriya, ta kafa wani kwamiti karkashin mataimakin shugaban kasar Yemi Osibanjo, wanda zai tattauna da bangaren 'yan majalisun kasar domin kawo karshen sabanin da bangarorin biyu ke samu.

Ministan cikin gida na Najeriya Janar Abdulrahaman Bello Dambazau
Ministan cikin gida na Najeriya Janar Abdulrahaman Bello Dambazau guardian.ng
Talla

Daga cikin manbobin kwamitin, akwai ministan kwadago Chris Ngige, ministan kasafin kudi da tsare tsare, Udoma Udoma, ministan sufurin jiragen sama Hadi Sirika, sai kuma Ministar ma’aikatar kula da mata Aisha Alhassan.

Sauran sun hada da mai bai wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari shawara kan sha’anin majalisar dattijai Ita Enang, sai kuma mai bai wa shugaban shawara, kan al’amuran majalisar wakilai, Alhaji Kawu Sumaila.

Yayin zantawarsa da sashin hausa na RFI, ministan cikin gida Janar Abdurrahman Bello Dambazau, ya ce samun sabani tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa a tsarin mulkin dimokaradiyya ba sabon abu bane.

A cewar ministan dan haka ne tilas ya dace a zauna domin gano bakin zaren matsalar idan aka yi la’akari da cewa dukkanin bangarorin biyu cigaban Najeriya suke nema.

01:00

NIGERIA-ABDURRAHMAN DAMBAZAU-1min-2017-03-30

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.