Boko Haram na fama da talauci- MDD
Majalisar Dinkin Duniya ta ce, kungiyar Boko Haram da aka karya lagwanta a Najeriya na fama talauci.
Wallafawa ranar:
Wani babban jami’in Majalisar Jeffery Feltman ya sanar da haka a yayin gabatar wa kwamitin tsaro da wani rahoto kan yadda Boko Haram ke barazana ga zaman lafiyar duniya.
Jami’in ya lura cewa, mayakan Boko Haram na fuskantar matsin lamba daga bangren sojoji, amma ya yi gargadi game da sakaci saboda yiwuwar kaddamar da sabbin hare-hare.
Mr. Feltman y ce, kungiyar Boko Haram na ci gaba da zama babbar barazana lura da tarin mayakan da take da su.
Sai dai matsalar rashin kudi da kuma rarrabuwar kawuna da ya tilasta wa kungiyar darewa gida biyu, na cikin abubuwan da ke kara durkusar da ayyukan kungiyar
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu