Gurbataccen wake ya haifar fargaba a Najeriya
A Najeriya yanzu haka jama’a sun fara nuna fargaba dangane da bayyanar wani gurbataccen wake a cikin kasuwanni musamman a jihar Gombe da ke arewa maso gabashin kasar, waken da ga alama aka sanya wa maganin kashe kwari domin ajiye shi na dogon lokaci. To sai dai daga bisani an sake fito da irin wannan wake a cikin kasuwanni, lamarin da ya sa jami’an kiwon lafiya da sauran hukumomin da ke kula da ingancin kaya ke gargadin jama’a da su yi taka-tsantsan. Wakilinmu Shehu Saulawa ya gudanar da bincike dangane da haka ga kuma rahotonsa.
Wallafawa ranar:
Gurbataccen wake ya haifar fargaba a Najeriya
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu