Isa ga babban shafi
Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta hallaka masu fashin shanu

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da hallaka ‘yan fashin 9 da kwato shanu 292 a kananan hukumomin Bungudu da Maru, a kokarin da take na raba Jihar Zamfara da barayin shanun da suka yi mata illa.

Jami'an sojin Najeriya
Jami'an sojin Najeriya
Talla

Daraktan yada labaran rundunar, Kanal Sani Usman Kukasheka, yace sun kuma kama ‘yan fashin guda biyu, tare da wani mai taimaka musu, da ake kira Abdullahi Abubakar wanda aka fi sani da Buharin Daji.

Kanal Usman ya ce adadin dabbobin da aka kwato sun kai shanu 292, raguna 44 da dokuna 17, yayin da aka lalata sansanin ‘yan fashin da baburan da suke amfani da su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.