Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Kaduna ta ce al'ummar Dangoma zasu dara

Yayin da Najeriya ke ci gaba da lalubo hanyoyin inganta tattalin arzikin kasar, Gwamnatin Jihar Kaduna ta sha alwashin ganin al’ummomin Dangoma da aka samu ma’adinin Nickel sun amfana da arzikin dake yankinsu.

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i via El rufa'is facebook page
Talla

Kwamishinan kula da Muhalli Malam Balarabe Shehu ya ce a halin da ake ciki gwamnatin jihar Kaduna tana kokarin ganin ta jawo ra’ayin masu zuba hannun jari a harkar hakar ma’adanai domin bunkasa tattalin arziki.

A cewar Malam Shehu lokaci yayi da al’ummar jihar Kaduna zasu samu bunkasar tattalin arziki don samun sauyin da aka shafe shekaru da dama ana nema.

Kwanishinan Muhallin ya sake jaddada kara dacewa gwamnatin jihar Kaduna zata tabbatar da cewa mutanen yankin Dangoma, inda aka samu sinadarin na Nickel sun amfana da cigaban.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.