Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram 26 a Dikwa

Rundunar sojin Najeriya ta ce, ta yi nasarar kashe mayakan Boko Haram 26 bayan yunkurin kaddamar da hari a sansanin ‘yan gudun hijra da ke karamar hukumar Dikwa a jihar Borno.

Mazauna sansanin Dikwa da ke jihar Borno a Najeriya
Mazauna sansanin Dikwa da ke jihar Borno a Najeriya STRINGER / AFP
Talla

To sai dai wasu majiyoyi sun ce, soja guda da jami’in ‘yan kato da gora guda har ma da wasu daga cikin mazauna sansanin na Dikwa sun rasa rayukansu a arangamar da ta kaure tsakanin sojojin da mayakan.

Wannan na zuwa bayan sojojin Najeriya sun karbe garin Kumshe da ke kan iyakar kasar da Kamaru daga hannun kungiyar Boko Haram.

Sama da ‘yan gudun hijra dubu 40 ke samun mafaka a sansanin na Dikwa wanda a baya ya gamu da hare haren Boko Haram da dama.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.