Isa ga babban shafi
Najeriya

Saraki ya mikawa Shugaba Buhari Sunanyen Ministocin da suka tantace

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Abubakar Bukola Saraki ya mikawa shugaban kasar Muhammadu Buhari sunayen ministocin da Majalisar ta tantance a fadar sa.

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Bukola Saraki
Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Bukola Saraki REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Saraki ya mika wa Shugaban takardar sunanyen ne tare da masu bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin majalisa wato Sanata Ita Enang da Abdurahman Kawu Sumaila.

Bayan kwarya-kwaryar bikin da aka yi a fadar, Saraki ya ce majalisar ta amince da duk kan mutane 36 da shugaban kasar ya aike mata domin nada su a matsayin ministoci.

A ranar 29 ga watan Oktoba, majalisar dattawan ta kammala tantance ministoci 36 da shugaba Buhari ya aika mata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.