Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram: 'Yan Sanda sun kama matasa 121 a Lagos

Jami’an 'Yan sandan Jihar Lagos da ke tarayyar Najeriya sun cafke wasu matsa kimamin 121 da suka fito daga birnin Kebbi na Arewacin kasar sakamakon zargin cewa suna da alaka da mayakan Kungiyar Boko Haram.

Ana zargin matasan cewa suna da alaka da Boko Haram.
Ana zargin matasan cewa suna da alaka da Boko Haram. S Martin/Flickr
Talla

To sai dai daya daga cikin ‘yan uwan matasan Abdullahi Umar Kawoje ya shaida wa RFI hausa cewa matasan ba su da alaka da Boko Haram kuma suna da sana’ar hannun da su ke yi a birnin Legas.

Kawoje ya kara da cewa an kama matasan ba tare da wani makami a jikinsu ba kuma akasarin su ba su kai shekarun balaga ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.