Isa ga babban shafi
Faransa

Hollande ya yi ikrarin kawo karshen matsalar basussukan kasashen Turai

Shugaban Faransa Francois Hollande ya yi ikirarin kawo karshen matsalar basukan kasashen Turai da ya addabi tattalin arzikinsu a tsawon shekaru hudu da suka gabata. Hollande ya yi wannan ikirarin ne a gaban manyan ‘Yan kasuwar kasar Japan lokacin da ya ke ziyara a kasar.

Shugaban Faransa, Fransois Hollande (hagu) tare da takwaransa, Shinzo Abe na Japan
Shugaban Faransa, Fransois Hollande (hagu) tare da takwaransa, Shinzo Abe na Japan REUTERS/Junko Kimura
Talla

A lokacin da ya ke jawabin bankwana a Japan, shugaba Hollande ya ce rikicin bashin Turai ya kasance wani tubali da ya karfafawa kasashen Turai samun kwarin gwiwar daukar matakan farfadowa.

Yawancin kasashen Turai dai suna fama da matsalar rashin ayyukan yi.

Haka kuma matsalolin dimbim bashin da ya addabi wasu kananan kasashen irin su Cyprus, wanda dole ta sa manyan kasashe suka tallafa wa kasar da bashin kudi euro Biliyan 10.

Wannan kuma na zuwa ne bayan warware rikicin bashin Girka da Ireland da Portugal da kuma Spain.

Shugaba Hollande dai ya ce yanzu sun dauki matakan ci gaban tattalin arzikinsu, wanda zai kasance mai dorewa, tare da yin alwakarin samar da ayyukan yi da ci gaban Faransawa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.