Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta umurci Kamfanin wutar Lantarki ya mayar wa al'ummar sokoto da Wuta

Babbar kotun Jahar Sokoto ta umurci kamfanin samar da wutar lantarki na kasa ya gaggauta mayar wa al’ummar Jahar da wuta. bayan wata kara da gwannatin Jahar ta shigar kan matakin da kamfanin ya dauka na katse bai wa jahar wuta saboda rikicinsu da ke tsakaninsu.

Gwamman Sokoto Alh Aliyu Magatakarda Wamakko
Gwamman Sokoto Alh Aliyu Magatakarda Wamakko thenation
Talla

A makon jiya ne hukumar samar da wutar Lantarki ta katse ba Jahar Sokoto hasken wutar lantarki bayan da wani wa'adi na sa'oi 48 da kungiyar ma'aikatan hukumar suka bai wa gwannan Jahar Aliyu Magatakarda Wamakko na ya aikewa hukumar takardar neman afuwa kan zargin dukan da ya yi wa wani ma'aikacin hukumar.

Wannan batu dai ya hifar da rudani a Jahar, kamar yadda wakilinmu Hassan Sahabi Sanyinnaswal, ya aiko mana da Rahoto.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.