Shirin Lafiya Jari Ce a wannan makon yayi maida hankali kan cutar gyambon ciki da ke addabar mutane musamman a yammacin nahiyar Afrika, da kuma matakan da ya dace a dauka don samun kariya daga kamuwa da cutar.
Sauran kashi-kashi
-
Yadda maza a Najeriya ba sa bai wa gwajin sankarar mafitsara mahimmanci
A wannan mako shirin ya mayar da hankali kan nau’ikan cutakan da ba a fiya mayar da hankali wajen yakarsu ba musamman a kasashe masu tasowa irin Najeriya, wannan nau’in cutuka kuwa sun kunshi kansar mafitsara ko kuma Prostate Cancer, nau’in kansar da ke matsayin mafi hadari ga maza, amma kuma ba ta samun kula duk da yadda ta ke kisan akalla mutum dubu 8 duk shekara a Najeriya.04/03/202410:00 -
Yawaitar gurbatattun jami'an lafiya a asibitocin Najeriya
A wannan makon shirin ya mayar da hankali kan yawaitar gurbatattun jami’an lafiya a asibitocin Najeriya wanda ke da nasaba da kodai rashin samun cikakken horo a kwalejojin lafiya ko kuma samun horon irin wadannan makarantu amma na bogi.A baya-bayan nan ana yawan ganin yadda ake bude tarin makarantu masu zaman kansu a sassan Najeriya da sunan horar da jami’an lafiya kama daga kwalejoji har da jami’o’I wadanda wasu daga cikinsu kan rasa sahalewar mahukuntan saboda rashin cancanta.29/01/202410:10 -
Najeriya ta fara amfani da fasahar tiyata ba tare da tsaga jiki ba
A wannan mako shirin ya mayar da hankali ne kan ci gaban da aka samu na fara amfani da fasahar fida ba tare da tsaga jikin majinyaci ba a Najeriya, a wani yunkuri na rage dogaro da kasashen ketare wajen irin wannan fida.18/12/202309:59 -
Najeriya za ta maida tsoffin likitoci bakin aiki domin cike gibin jami'an lafiya
Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wanna makon tare da Murtala Adamu Ibarhim ya maida hankali ne kan shirin gwamnatin Najeriya na sake daukar likitoci da sauran jami'an kiwon lafiya wadanda suka yi ritaya daga aiki, a wani kokari na cike gibin karancin jami'an kiwon lafiya a kasar, masamman guraben wadanda suka tsere zuwa kasashen waje domin samun albashi mai soka.13/11/202309:57 -
Yadda ake gano cutar koda da kuma hanyar magacen ta ( Kashi na 2)
Shirin Lafiya Jari Ce na wannan makon ya tattauna ne kan musabbabin kamuwa da ciwon koda a daidai lokacin da wasu alkaluma ke nuni da cewa, akwai mutane kimanin miliyan 17 da ke fama da cutar a Najeriya.26/10/202309:53