Isa ga babban shafi
China/Sin

Amurka na fatan karfafa dangantaka tsakaninta da sabuwar gwamnatin Sin

Kasar Amurka tayi fatan ganin dangantaka tsakanin ta da sabuwar Gwamnatin kasar Sin ya kara karfi wajen warware matsalolin da suka shafi duniya baki daya. Jim kadan da bayyana sabuwar Gwamnatin kasar China ne dai, karkashin Shugaba Xi Jinping, Tom Donilon, Mashawarcin Amurka ta fannin tsaro, ya mikawa China sakon fatan alheri a madadin Shugaban Barack Obama, inda yake fatan dorewar dangantaka mai amfani. 

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama Reuters
Talla

A cewar Donilon, akwai yanayi mai kyau domin dorewar zumunci tsakanin kasashen biyu, inda yayi fatan China zata rika tafiya daidai da zamani, ganin yadda take hawa kujeran naki, gameda batun kasar Korea ta Arewa, da batun kasar Iran, da zance dumamar yanayi da dai batun tattalin arzikin na duniya.

Shi dai wanna Babban Mashawarcin tsaro da ake ganin yana iya maye gulbin Sakatariyar waje na Amurka Hillary Clinton, saboda rawar daya taka wajen dorewar dangantaka tsakanin Amurka da China.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.