Isa ga babban shafi
Turai

Kungiyar Kasashen Turai na tunanin haramtawa kanfanonin dake sa ido kan hada hadar kudade

Kungiyar Kasashen Turai na tunanin haramtawa kanfanonin dake sa ido kan hada hadar kudade da basusuka bada rahotan kan kasashen su, ganin yadda rahotan ke yin illa.Ganin irin rahotanin kanfanonin sa idon irin na Moody, Standard and Poor, da Fitch, ke jefa kasashen Turai da kuma tattalin arzikin duniya cikin rudani, kungiyar kasashen Turai yanzu haka ta tsara wani daftarin da zai baiwa Hukumar dake kula da kasuwancin Turai damar haramtawa kasashen gabatar da irin wannan rohoto a bainar jama’a.Rahotanni sun ce, kwamishinan kula da kasuwanni na kungiyar, Michel Barnier, ya bayyana haka, ganin yadda rahotanni suka jefa wasu kasashen Turai cikin halin kakanikayi.'Yan siyasa a Turai na zargin wadanan kanfanoni da bada bayanan da ba haka suke ba akan kasahse, abinda ke dada tabarbarewar al’amura.Ko a cikin wannan mako sai da kanfanonin suka rage darajar basusukan Faransa, Spain, da Italiya.  

Reuters/Remote/Pawel Kopczysnki
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.